A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Ahmad Abidi, a yayin tunawa da shahadar Sayyida Fatima Ma’asuma (S), ya yi bayani kan matsayinta mai girma da kuma rawar da kasancewarta a Qum ta taka wajen ɗaukaka matsayin ilimi da ruhaniya na wannan birni. Ga cikakken bayanin wannan malamin na Hauza:
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin ƙai
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu kuma Annabinmu, masoyin Ubangijin talikai, Abul-Qasim Muhammad (S), da zuriyarsa tsarkaka, musamman hujjar Allah a doron ƙasa, rayukanmu su zama fansa ga ƙurar sawunsa.
Assalamu alaiki ya ’yar Manzon Allah, assalamu alaiki ya ’yar Sarkin Muminai, assalamu alaiki ya ’yar Hasan da Husaini, assalamu alaiki ya ’yar Musa bn Ja’afar, da rahamar Allah da albarkarsa.
Sunan asalin Sayyida Ma’asuma (S)
Sayyida Fatima Ma’asuma (S), sunanta na asali shi ne “Sitti”. A zamaninta, mutane sun fi saninta da wannan suna na “Sitti”. Makarantar “Sittiyya” ma saboda wannan ne aka danganta sunanta da ita.
An ambaci sunan “Sittiyya” sau da yawa a cikin tsoffin littattafan tarihi. Idan aka ambaci sunan wannan baiwar Allah mai daraja, ana kiran ta da “Sitti ’yar Musa bn Ja’afar (AS)”.
Sayyida Ma’asuma (S) ita ce abin alfahari na ƙasar Iran, musamman birnin Qum. Duk girma da ɗaukakar Qum, ta fuskar al’adu, gine-gine da sauran fannoni, suna da alaƙa da albarkar Sayyida Ma’asuma (S).
Sayyida Ma’asuma (S) ta yaɗa al’adun Shi’a da koyarwar Ahlul Baiti a Qum, sannan daga Qum zuwa sauran sassan Iran. A hakikanin gaskiya, dukkanmu ta wata hanya muna ɗauke da bashin Sayyida Ma’asuma (S) saboda irin gudunmawar da ta bayar.
Mutanen Qum ma suna da wata muhimmiyar al’ada ta girmama Sayyida Ma’asuma. Wurin da muke zaune a yanzu, a zamanin da ana kiransa “Bagh-e Babulan” (Lambun Babulan). Bayan shahadar Sayyida Ma’asuma, an kawo ta wannan wuri, wato Bagh-e Babulan, aka binne ta a nan. Tun daga wannan lokaci, wurin ya kasance wajen binne mutane.
Amma girmamawar da mutanen Qum suke yi wa Sayyida Ma’asuma ta kai matsayin da ba sa binne wani namiji a kusa da ita. Matan da ake binnewa a wannan wuri sukan kasance daga cikin zuriyar Manzon Allah, wato Sharifai, ko kuma mata masu daraja.
Har zuwa kusan ƙarni huɗu da suka gabata, aka fara binne wasu manyan malamai, maraji’an addini, sarakuna, ministoci da wasu manyan mutane a cikin Haramin. Duk da haka, a lokacin da aka fara yin hakan, ba a binne wani namiji da ba muharrami ba kusa da Sayyida Ma’asuma.
Ko da yake a mahangar Fiƙihu babu wata matsala idan aka binne mamacin namiji da mace kusa da juna, amma girmamawar da mutanen Qum suke yi wa Sayyida Ma’asuma ta kasance mai girma matuƙa, har ba sa binne wani namiji a ƙarƙashin kubbar Haramin Sayyida Ma’asuma ko kusa da kabarinta mai albarka. Idan kuma za a binne mace, dole ta kasance Sharifiya ko kuma mace mai daraja.
Wannan yana nuna irin yadda mutanen Qum suke girmama mata, musamman matan da suke daga zuriyar Manzon Allah (S), tare da ba su matsayi, daraja da kima.
Manzon Allah (S) a wani daga cikin yaƙe-yaƙe ya ga Musulmi sun kashe wata mace kafira. Bisa wannan ruwaya, Manzon Allah (S) ya ce:
«قاتلکم الله،إنها لا تقاتل»
“Qatalakumullahu, innaha la tuqaatil” Ma’ana: “Allah Ya halaka ku! Me ya sa kuka kashe wannan matar? Ita ba ta yaƙi.”
Wannan yana nuna cewa al’adar Manzon Allah da koyarwar addininmu ita ce girmama mace matuƙa. A wata ruwaya, Manzon Allah (S) ya ce:
«ما أکرم النساء إلا کریم و لا أهانَهُن إلا لئیم»
Ma’ana: “Babu wanda yake girmama mata face mutum mai daraja, kuma babu wanda yake wulaƙanta su face mutum marar daraja da mummunan hali.”
A nan Manzon Allah (S) bai ce mace Musulma ko wadda ba Musulma ba. Ya faɗi mace gaba ɗaya. Ma’ana, mace tana da daraja, kuma wannan shi ne tsarin koyarwar addininmu.
Wannan girmamawar da muke yi wa Sayyida Ma’asuma (S) ita ce har dukkan Maraji’anmu suna nuna ladabi da girmamawa a gaban Sayyida Fatima Ma’asuma (S). Wannan shi ne gaskiya da ruhin addininmu.
Ku kuma kwatanta wannan da abin da waɗannan ‘yan mamayar Sahayoniyawa suke yi, waɗanda a cikin wannan shekara suka kashe sama da mata Musulmi dubu goma sha ɗaya. Manzon Allah (S) ya la’anci Musulmin da ya kashe mace kafira. Waɗannan Yahudawa da Sahayoniyawa sun kashe mata dubu goma sha ɗaya marasa laifi, waɗanda babu ɗayansu da ta je yaƙi, suna zaune ne a gidajensu. Saboda haka, ya kamata a la’anci waɗannan Sahayoniyawa da masu mamaya sau dubu goma sha ɗaya da ma dubbai.
Siffofin Sayyida Ma’asuma (S)
Sayyida Fatima Ma’asuma (S) tana da siffofi da yawa, amma zan faɗi abu guda ne kawai. Sayyida Ma’asuma ta rayu a rabin ƙarni na biyu bayan hijira, wato a lokacin da yanayin al’adu da addini a ƙasashen Musulmi ya kasance cikin wani hali da zan yi bayani a kansa. Ku duba irin manyan ayyukan da Sayyida Fatima Ma’asuma (S) ta yi wa duniyar Musulmi.
A zamanin Harunar-Rashid da Ma’amun, har Musulmi sun kai matsayin da suke shakku kan ko giya haram ce ko halal. Wato an yi yaƙin neman gurbin al’adun Musulunci ta yadda wani mutum mai suna Mahdi al-Abbasi, wanda yake da matsayi a gwamnati, ya zo yana cewa babu wata hujja da ke nuna cewa giya haram ce, har ma yana yaɗa shan giya a cikin al’ummar Musulmi.
Allama Majlisi, Allah Ya jiƙansa, ya kawo ruwayoyi da dama a cikin littafin Biharul-Anwar, wadanda suka bayyana yadda Imam Musa bn Ja’afar (AS) yake bayanin haramcin giya ga mutanen da idan suka ji hakan suke cewa: “Ba mu taɓa jin cewa giya haram ce ba.”
Wannan yana nuna yadda lamarin ya lalace. Kiɗa, fasikanci, barin sallah, rashin kunya da rashin kamun kai, da sauran irin waɗannan abubuwa sun yaɗu matuƙa a cikin al’umma.
Ɗaya daga cikin ayyukan Harunar-Rashid da Ma’amun shi ne yaɗa addinan da suka kauce daga gaskiya a cikin al’umma. Misali, waɗanda ake kira Khurramiyya ko Mazdakiyya, waɗanda a yanzu ake danganta su da Babak Khorramdin, wadanda abin takaici har yanzu ana gudanar da wasu bukukuwa a arewacin ƙasar Iran, tushen wannan ƙungiya ya samo asali ne daga wancan zamani. A wancan lokacin ne aka yaɗa Khurramiyya, da kuma Sabians da makamantansu.
A zamanin Sayyida Fatima Ma’asuma (S), yanayin akhlaƙ, al’adu da ilimi ya shiga wani mummunan koma baya. Akwai malamai da dama, amma a wancan lokaci ana shagaltar da su da abubuwan da ba su da amfani.
Ku duba, alal misali, a zamanin Jamal Abdul Nasser, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake mayar da hankali a kai a birnin Alkahira da Masar shi ne binciken tushen wata kalma. Wani lokaci ma ana sanya kyautar rakuma ɗari ko dubu ga wanda ya gano tushen wata kalma. A lokacin da duniyar Musulmi take fuskantar Yahudawa, mamayar ƙasashen Musulmi da zubar da jinin marasa laifi, su kuma suna shagaltuwa da binciken tushen wata kalma.
Haka abin yake a zamanin Harunar-Rashid. Yana tattara mutane da malamai, ya shagaltar da su da wasu batutuwan ilimi waɗanda ba su da wani tasiri a cikin al’umma. Wannan ma dogon labari ne.
Matsayin ilimin Sayyida Ma’asuma (S)
Amma me Sayyida Fatima Ma’asuma (S) ta yi a cikin irin wannan yanayi? Wataƙila da yawa daga cikinku kun taɓa jin wannan labari.
Wata tawaga ta zo Madina domin zuwa wajen Imami na bakwai, wato Imam Musa bn Ja’afar (AS), domin su tambaye shi wata tambayar Fiƙihu. A wancan lokaci babu waya da sauran hanyoyin sadarwa na zamani.
Da suka zo Madina, sai suka gano cewa Imam Musa bn Ja’afar (AS) ya yi tafiya kuma baya Madina. Hakan ya ba su haushi, domin sun yi doguwar tafiya ne domin su tambayi Imam, amma sai suka tarar ba ya nan.
Sai suka je gidan Imami na bakwai. Wata yarinya ta fito, wadda wataƙila tana da shekaru bakwai kawai. Ita ce Fatima Ma’asuma (S).
Ta tambaye su: “Me ya kawo ku?” Suka ce: “Muna da wasu tambayoyi da muke son yi wa mahaifinku.” Sayyida Ma’asuma ta ce musu: “Ku rubuta tambayoyinku ku ba ni.”
Sai suka rubuta tambayoyinsu, ita kuma ta rubuta amsoshin a gabansu. Lokacin da suka karɓi amsoshin, ba su iya yarda ba. Sun ga cewa wata yarinya ’yar shekara bakwai ce ta ba da amsoshin tambayoyin Fiƙihu. Sun karɓi amsoshin, amma har yanzu suna shakku ko amsoshin daidai ne.
Suka bar Madina suna komawa gidajensu. A cikin jeji suna tafiya, sai suka ga wata tawaga tana zuwa. A cikin wannan tawaga kuwa akwai Imam Musa bn Ja’afar (AS). Suka yi farin ciki matuƙa. Suka ce: “Ya ɗan Manzon Allah! Muna da wasu tambayoyi da muka zo domin mu tambaye ku. Mun je gidanku, amma ba ku nan. Sai wata yarinya ta fito ta rubuta mana wasu amsoshi.”
Imam (AS) ya ce: “Ku ba ni in gani.” Sai suka ba shi takardar da Sayyida Ma’asuma (S) ta rubuta. Imam Musa bn Ja’afar (AS) ya karanta ta, sannan ya ce: “Fidaha abuha” — “Mahaifinta ya zama fansarta.”
Ta wannan hanya, Imam (AS) ya tabbatar da matsayin ilimin Sayyida Ma’asuma (S), ya tabbatar da ingancin amsoshinta, sannan ya ƙarfafa gwiwar waɗanda suka zo da tambayoyin.
Wannan yana nuna cewa tun daga ƙuruciyarta, Sayyida Fatima Ma’asuma (S) tana da wannan matsayi na ilimi. Wataƙila wannan ba ilimi irin na yau da kullum ba ne; ko kuma ilimi ne na musamman. Amma duk wanda ya samu damar kasancewa tare da Imam na bakwai da Imam na takwas (AS), zai iya kaiwa irin wannan matsayi mai girma na ilimi da sani.
Wannan shi ne matsayinta na ilimi.
Gudunmawarta wajen yaɗa kamun kai da akhlaƙ
Amma abin da ya fi wannan muhimmanci shi ne Sayyida Ma’asuma (S) ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa kamun kai, kunya da nisantar alfasha da munanan ayyuka.
Ɗaya daga cikin siffofin Imam Musa bn Ja’afar (AS) ita ce “sirrin Musa bn Ja’afar”, wato irin taimakon da yake bayarwa a ɓoye, wanda aka yawaita ambatonsa a cikin littattafan tarihi.
Ko kun taɓa jin labarin wannan taimako na sirri da Imam Musa bn Ja’afar (AS) yake yi? (Shahidin) Jagoran Jamhuriyar Musulunci ma ya taɓa ambatonsa a cikin wasu jawabansa.
Daga ina Imam na bakwai yake samun waɗannan kuɗaɗe? Ta yaya yake kashe jakunkunan kuɗin da yake bayarwa? Daga ina yake samun waɗannan kuɗaɗe? Wannan ma dogon labari ne. Amma galibi ana amfani da waɗannan kuɗaɗe ne wajen yaɗa akhlaƙ da ruhaniya.
Ruhaniya a matsayin hanyar fuskantar matsalolin rayuwa
Wani daga cikin siffofin Sayyida Ma’asuma (S) shi ne yadda take koya mana cewa rayuwa kullum tana tare da wahala. Kowane mutum yana fuskantar matsaloli a rayuwarsa; ko matsalar yaƙi ce, rashin tsaro, matsalar iyali, ’ya’ya da makamantansu.
Turawan Yamma suna cewa hanyar yaƙar irin waɗannan matsaloli ita ce abubuwa kamar kiɗa, alfasha da munanan ayyuka, hotunan batsa da makamantansu, domin su shagaltar da mutum daga matsalolin da yake fuskanta a rayuwa.
Wannan shi ne abin da suke ganin mafita ce, har a titunansu ake sanya alluna da hotuna marasa kyau domin mutane su kalle su, su manta da wahalhalun rayuwa.
Amma addininmu da al’adarmu, abin da Sayyida Ma’asuma (S) ta yaɗa shi ne cewa ana iya fuskantar matsalolin rayuwa ne ta hanyar zuhudu, ruhaniya, kyawawan ɗabi’u, kusanci da Allah, ibada, biyayya da neman taimako daga Allah da Ahlul Baiti.
Abubuwan da Turawan Yamma suke gabatarwa a matsayin mafita ga matsaloli, a zahiri mafita ce ta ɗan lokaci, wato guduwa ne daga wahala, ba warware wahalar ba.
Amma abin da yake cikin makarantar Imam Musa bn Ja’afar (AS) shi ne cewa sallah, ibada, tawassuli, kuka, gyaran ɗabi’a, wa’azi da nasiha su ne hanyoyin asali na magance matsalolin. Sauran abubuwa kuwa suna matsayin na gefe ne kuma na ƙari.
Sayyida Ma’asuma (S) maruwaiciyar Hadisi ce
Wani abu na ƙarshe da zan ambata game da Sayyida Fatima Ma’asuma (S) shi ne cewa ita Muhaddisa ce, wato ita ma mai ruwayar Hadisi ce.
Abu mai ban sha’awa shi ne cewa Sayyida Ma’asuma (S) galibi ba ta riwaya daga maza. Ruwayoyin Hadisinta waɗanda isnadinsu ya kai ga Manzon Allah (S), dukkan jerin masu ruwayar suna mata ne. Wato daga mata zuwa mata ne. Wannan yana nuna cewa tana cikin makarantar mata, kuma tana gudanar da ayyukan al’adu da ilimi tare da mata.
Abu mafi ban sha’awa kuma shi ne cewa dukkan batutuwan Hadisan da Sayyida Ma’asuma (S) ta riwaya suna da alaƙa da Wilayar Amirul Muminin Ali (AS) da kuma Musulunci na gaskiya wanda Ahlul Baiti (AS) suka koyar.
A ƙarshe, Fatima Ma’asuma (S) ita ce mafi kyawun mace a zamaninta.
Manzon Allah (S), bisa wata ruwaya, ya ce:
«خَیرُکُم خَیرُکُم لأَهلِهِ و َأَنَا خَیرُکُم»
Ma’ana: “Mafi alherinku shi ne wanda ya fi alheri ga iyalinsa, kuma ni ne mafi alherinku.”
Manzon Allah (S) ya faɗi haka domin shi ne wanda ya fi kowa girmama matansa da yi musu karamci.
Matar Manzon Allah (S) A’isha ta ce, ba a taɓa samun lokacin da Manzon Allah (S) ya fita daga gida ba tare da ya ambaci wata kyakkyawar magana game da Sayyida Khadija (S) ba. Haka kuma ba a taɓa samun lokacin da ya dawo gida ba tare da ya sake yabon Sayyida Khadija (S) ba. Saboda yawan ambatonta, A’isha ta kasance tana nuna rashin jin daɗi da korafi, tana cewa me ya sa yake yawan yabon ta haka.
Amma Sayyida Khadija (S) ita ce wadda a karo na farko da Jibrilu (AS) ya sauko wajen Manzon Allah (S), ya ce masa: “Ina isar maka da sallamar Allah zuwa ga Khadija.”
Manzon Allah (S) ya ce: “Ni ne mafi alherinku, domin ni ne na fi kowa girmama matana.”
Saboda haka, mu ma idan muka ƙara girmama matanmu, iyalanmu da mata gaba ɗaya, wannan yana daga cikin al’adun da Sayyida Ma’asuma (S) ta koyar.
Waɗannan su ne alamomin alheri, kamala da darajar mutum.
Ra'ayinka